OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Jam'iyar Labour A Gombe Ta Nemi Mata Da Su Zaɓi Peter Obi

2023: Jam'iyar Labour A Gombe Ta Nemi Mata Da Su Zaɓi Peter

Shugabar mata na jam’iyyar Labour ta ƙasa, Dugu Manuga ta ce buƙaci mata da su zaɓi Peter Obi don ganin ya ɗare mulkin ƙasar nan.

Da take jawabi yayin taron gangamin ƙungiyar mata ta jihar da aka gudanar a Gombe domin wayar da kan ƙungiyoyi gabanin zaɓen 2023, Manuga, ta tunatar da su irin ƙarfin da suke da shi a nasarar ƴan takara.

A cewar Manuga, akwai buƙatar mata su haɗa ƙarfi da gwiwa da kuma kare aikinsu, tana mai jaddada cewa in ba haka ba burin Obi ba zai tabbata ba.

Wakilin Jaridar Punch ta ruwaito cewa taron ya kuma gabatar da rahotannin shugabannin mata daga kananan hukumomin Akko da Yalmatu Deba.

Ta ce ba tare da haka ba sakamakon na iya yin tasiri a kan ɗan takarar jam'iyyar.

“Dole ne mu ɗauki nauyi kuma mu tabbatar mun yi abin da ya kamata mu yi, domin jam’iyyar Labour za ta fito cikin nasara a Gombe da ma ƙasa baki daya."

Yayin da take yabawa Obi, musamman yadda mata suka shiga yaƙin neman zaɓen shi, Manuga ta ce Obi zai cika kashi 35 cikin ɗari na bawa mata muƙamai.

“Peter Obi yace zai baiwa mata muƙamai kashi 35-40.  

"Ba zai zama kasa da kashi 35 ba, Ku tuna lokacin da yake gwamnan jihar Anambra, ya bawa mata kashi 40."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci