OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Majalisar Wakilai Ta Umarci Bankin CBN Ya Dakatar Da Sayar Da Bankin Polaris

Majalisar Wakilai Ta Umarci Bankin CBN Ya Dakatar Da Sayar D

Polaris Bank

Majalisar wakilai ta umarci babban bankin Najeriya CBN da ya gaggauta dakatar da siyar da bankin Polaris Plc.

 

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa Henry Nwauba, (APGA-Imo), ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba.

​​​​

Ya ce an jawo hankalin jamaa ta hanyar yada bayani a shafukan sada zumunta kan batun sayar da bankin Polaris kan Naira biliyan 40.

​​​​​​

Ya ce ya kamata a tabbatar da cewa saida bankin ba zai kawo cikas ga kasuwancin da ke gudana tsakanin sa da CBN ba domin amfanin alumma gaba daya.

​​​​​​

Ya ce hakan ya zama dole domin kaucewa korafe-korafen jamaa game da rashin mayar da martani daga masu ruwa da tsaki a harkar tattalin arziki, abokan huldar kasuwanci na kasashen waje ta hanyar hulda da bankuna.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci