OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Goje ya kaddamar da samar da wutar lantarki da makarantu a mazabar sa

Goje ya kaddamar da samar da wutar lantarki da makarantu a m

Senator Danjuma Goje

Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Muhammad Danjuma Goje ya fara aikin samar da wutar lantarki a kauyuka 23 a kananan hukumomin Akko da Yamaltu Deba na jihar Gombe.

Goje ya kuma bayyana cewa zai gina ajujuwa guda goma sha uku a cikin kauyuka 26 na kananan hukumomin biyu.

Goje ya bayyana haka ne yayin kaddamar da aikin a kauyukan Lawanti da Shinga a karshen makon da ta gabata. 

Ya ce nan ba da jimawa ba za a dawo da wutar lantarki a cikin kauyukan. 

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, a cewar sa, galibin kauyukan sun samu wuta ne daga lokacin yana gwamna ko kuma ministan wutar lantarki.

Yayin da yake bayanin dalilin da ya sa kauyukan suka ci gaba da kasancewa cikin duhu, ya ce hakan na faruwa ne “saboda rashin na’urar taransifoma, rashin layukan wutar lantarki ko kuma tsinkewar wayoyin da ke isar da wutar ga kauyukan.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci