OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gobara Ta Kama Ofishin WAEC Na Ƙasa Dake Legas

Gobara Ta Kama Ofishin WAEC Na Ƙasa Dake Legas

Rahotanni sun bayyana cewa ofishin hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta yammacin Afirka (WAEC) da ke garin Yaba ya ƙone ƙurmus a safiyar yau Laraba.

A cewar gidan rediyon Legas Bond FM, jami’an kashe gobara na jami’ar Legas (UNILAG) da kwalejin fasaha ta Yaba (YABATECH) sun isa wurin domin kashe gobarar.

Wani ganau ya bayyana cewa an ga wasu ma’aikatan ma'aikatar da ake kyautata zaton sun maƙale ne a tsakanin benaye suna yunƙurin dirowa ta tagar ginin mai hawa 12 domin tsira da rayuwarsu.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu daya daga cikin jami’an ma'aikatar da ya ce uffan akan lamarin.

Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a yankin Kudu-maso-Yamma, Ibrahim Farinloye, ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa wata gobara ce ta ɓarke, kuma tuni aka kashe gobarar.

An ruwaito cewa jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) ma an tura su wurin da lamarin ya faru.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Shakiru Ahmadu, ya ce an ceto mutane bakwai daga ginin.

Babban sakataren hukumar LASEMA, Dakta Olufemi Oke-Osanyintolu, ya ce gobarar ta tashi ne daga hawa na uku na ginin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci