OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Wani hatsarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutum biyu a Jigar Ogun

Wani hatsarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutum biyu a Jigar

Wani hatsari da ya afku a mahadar Idogo dake kan titin Ilaro-Owode Yewa a jihar Ogun ya yi sanadin mutuwar mutane biyu. 

 

Haka kuma, mutum guda ya samu munanan raunuka a hatsarin wanda ya afku a ranar Juma'a.

 

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar kiyaye hadurra ta jihar Ogun ta yi barazanar fara kama masu ababen hawa da ke ajiye motoci ba gaira ba dalili a kan tituna.

 

Rahotanni sun ce hadarin ya hada da wata mota kirar Mitsubishi mai lamba JJJ168JF da wata babbar mota mai lamba T12224LA. Motar da ake zargin tana da gudu sosai, an ce ta fada kan babbar motar da aka ajjiye a gefen hanya ba bisa kaida ba.

 

Mai magana da yawun rundunar, Florence Okpe, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a.

 

 Wadanda suka jikkata da gawarwakin an mika su zuwa babban asibiti da kuma asibitin Hosanna da ke Ilaro. 

 

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “jami'an hukumar kiyaye afkuwar hadura ta FRSC sun ceto wadanda hatsari ya rutsa dasu a hanyar Ilaro-Owode da ke kusa da Iyana Odogo wanda ya faru da misalin karfe 0600.

Hadarin ya hada da motoci guda biyu: Motar Mitsubishi mai lamba JJJ854JH da wata babbar mota kirar T12224LA. Mutane bakwai ne a cikin motocin maza hudu da mata uku, sai kuma mace daya ta samu rauni yayin da maza biyu suka mutu a hadarin. Abubuwan da ake zargin sun haddasa hadarin sun hada da gudun wuce sa'a da ajjiye mota ba bisa ka'ida ba."

 

 A halin da ake ciki, Kwamandan Rundunar FRSC ta Jihar Ogun, Anthony Uga, ya bayar da umarnin cewa, daga yanzu rundunar ta fara binciken wuraren ajiye motoci kuma duk wanda aka samu yana aikata irin wannan laifin to ya fuskanci fushin doka.

 

 Ya kuma shawarci masu ababen hawa da su rika tuka mota bisa tsari da ka’ida, sukuma gujewa yin gudun wuce sa'a.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci