OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

EFCC Tayi Ram Da Dan Bautan Kasa Da Wasu 18 Kan Laifin Damfarar Yanar Gizo a Lokoja

EFCC Tayi Ram Da Dan Bautan Kasa Da Wasu 18 Kan Laifin Damfa

Hukumar EFCC ta cafke wani dan bautan kasa da wasu mutane 18 da ke damfarar yanar gizo wanda aka fi sani da ‘yahoo-yahoo’.

Jami’an hukumar EFCC shiyyar Ilorin ne suka kama wadanda ake zargin a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

A cewar sanarwar da EFCC ta fitar a shafinta na Facebook, an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan rahoton sirri da aka samu a karshen makon da ta gabata. 

Mutanen 19 da ake zargin sun hada da Adamu Shuaibu, dan bautan kasa wato NYSC. 

Sauran mutane goma sha takwas da ake zargin sun hada da: “Achimugu Nelson Ojonoka, Victor Atsumbe, Akoh Grace Samuel, Usman Abubakar Sadiq, Jacob Emmanuel, Solomon John, Christian Oyakhilome, Adesanya Adeolu Tosin, Uloko George Ojonugwa da Timothy Eleojo Moses.

“Sauran sun hada da Negedu Joseph Onuchei, Usman Tenimu, Lukman Musa, Samuel Atadoga, Daniel Atekojo James, Abdulrazaq Iko-ojo Ahnod, Olarewaju John Olumide da Ademola Adegoke Daniel,” kamar yadda sanarwar ta karanta.

Kayayyakin da aka samu lokacin kamen sun hada da makudan kudade da ake zargin sun samu ne daga haramtattun ayyukansu da wata mota kirar Lexus.

Sauran abubuwan da aka gano sun hada da nau'ikan wayoyi daban-daban, kwamfyutocin tafi-da-gidanka da sauran abubuwan da ke tambatar da aika-aikan su. 

Sanarwar ta kuma bayyana cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar shari’a da zarar hukumar ta kammala bincike.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci