OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Da Duminsa: EFCC Ta Kama Daraktan Asusun NDDC Kan Badakalar Naira Biliyan 25

Da Duminsa: EFCC Ta Kama Daraktan Asusun NDDC Kan Badakalar

Jami’an Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta damke Daraktan Kudi da Akanta na Hukumar raya Neja Delta (NDDC), Mista Eno Ubi Otu.

Rahotanni sun ce jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun kama Otu ne da misalin karfe 11:15 na safe dangane da zargin karkatar da kudaden haraji sama da Naira biliyan 25.

Wata majiya a Hukumar ta shaida wa Jaridar Daily Trust cewa har yanzu jami’in NDDC na tare da jami’an da misalin karfe 7:15 na yamma lokacin da aka gabatar da wannan rahoto.

A cewar jami’in, kama Otu ya kasance wani babban bincike na rahoton binciken kwakwaf na NDDC.

Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun Hukumar, Wilson Uwujaren ya ci tura, yayin da kokarin kiran wayarsa ya yaci tura.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci