OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Dole Duk Wanda Ya Cancanta Ya Biya Haraji A Najeriya - Buhari

Dole Duk Wanda Ya Cancanta Ya Biya Haraji A Najeriya - Buhar

Shugaban Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce gwamnatin sa na ƙara ƙaimi wajen ganin duk ƴan ƙasar suna biyan haraji.

Shugaban wanda yace masu karbar haraji zasu bayyana kuɗaɗen da suke samu tare da biyan harajin da ya dace ga hukumomin da suka dace.

Buharu ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da yake miƙa kasafin kudin shekarar 2023 ga taron hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta ƙasa a Abuja.

Shugaban yayin miƙa kasafin da yakai Naira Tiriliyon 20.52 ya bayyana  karancin kuɗaɗen shiga a matsayin babbar barazana ga harkokin kasafin kudin Najeriya.

“Rashin kuɗaɗen shiga ya kasance babbar barazana ga tattalin arzikin Najeriya.  

"Don haka mun ƙara ƙaimi wajen tabbatar da cewa duk ƴan Najeriya masu biyan haraji sun bayyana kudaden shiga daga kowane tushe da kuma biyan haraji saboda hukumomin da suka dace.

"Muna kuma sanya ido kan kuɗaɗen shigar da hukumomin gwamnati ke samu a cikin gida don tabbatar da an yi musu lissafin yadda ya kamata su buya," in ji shi.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Buhari na cewa ya yi farin cikin bayar da rahoton cewa sauye-sauyen tattara kuɗaɗen shiga da kashe kuɗaɗe na samar da sakamako mai kyau. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci