OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Direbobin Keke Napep A Kaduna Sun Koka Kan Yawan Haraji

Direbobin Keke Napep A Kaduna Sun Koka Kan Yawan Haraji

Direbobin Keke Napep sun koka kan yawan karbar haraji da kungiyoyin sufuri da gwamnati ke tallafawa a jihar Kaduna ke yi.

Direbobin da suka koka yayin da suke zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a yau, sun ce yawan harajin da ake karba ya sanya aikin su ya yi wahala.

Wani direban mai suna David Akin ya ce yana biyan akalla N2500 a kullum.

Akin ya ce: “Kungiyoyi daban-daban za su buga rasit kawai kuma za ku ga yara maza da ba su da ɗabi’a suna tursasa mu yayin da muke ƙoƙarin samun abin dogaro.

"Zan so gwamnati ta shiga tsakani ta hanyar daidaita duk wadannan kungiyoyin zuwa ga hukuma daya domin mu san inda harajin mu zai je."

Wasu daga cikin su sun yi korafin cewa ba za su iya cika kudin da akace su biya masu kekunan ba saboda yawan harajin da ake karba wanda zai iya haifar musu da matsala da masu Keke Napep din. 

Wani Yusuf Nda ya kuma ce, “Za ku ci karo da wata kungiyar da za ta bukaci Naira 100, N1000, N4,000 na tikitin karamar hukuma, sitika ko rajistar fenti.

"Wannan halin da ake ciki shi ne ya sa muka kara kudin tafiya, kuma za mu so gwamnatin jihar ta sa baki domin wadannan kudaden harajin su daina."

A cewar shugaban wata kungiyar, Kadsico Unit Union, Shegun Samuel ya tabbatar da cewa jihar tana da kungiyoyi sama da goma inda kowacce ke ikirarin ita ce ta fi inganci.

Samuel ya bayyana cewa: “Abin takaici, yayin da masu Keke Napep din ke shan wahala, ita ma gwamnatin jihar ba ta samun isassun kudaden shiga saboda yawaitar wadannan kungiyoyin.

“Idan ka je wasu jihohi, kungiya daya ce kawai suke da su amma saboda son kai na wasu mutane sai su je su shirya kansu su buga rasit”.

A halin da ake ciki wani jigo a hukumar tattara kudaden shiga ta jihar wanda ya nemi a sakaya sunan sa ya ce kungiyar ita ce ke kula da harajin rajistar motoci da kuma bayanai, yana mai jaddada cewa: “Akwai kuma Naira 100 da matuka ke biya a kullum, baya ga wannan, duk sauran kungiyoyin da ke karbar haraji suna aiki ne ba wanda yasa su.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci