OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Dalilin Da Ya Sa Ba Za Mu Iya Kara Albashin Ma’aikata Ba – Buhari

Dalilin Da Ya Sa Ba Za Mu Iya Kara Albashin Ma’aikata Ba �

Shugaban Ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana dalilan da suka sa gwamnatin tarayya ta gaza ƙara albashin ma’aikatan gwamnati duk da bukatar hakan.

A wata sanarwa da mai taken ‘ Shugaba Buhari ya tabbatar da Rahoton Oronsaye zai haifar da sauye-sauye a ma’aikatan gwamnati', wacce mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar, ta ruwaito Buhari na bayyana dalilan a lokacin da ya karbi baƙuncin kwamitin ƙungiyar manyan ma’aikatan gwamnati a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Da yake mayar da martani kan buƙatar kwamitin na duba albashin ma’aikata, shugaban ƙasar ya ce yayin da ake buƙatar yin wannan bita cikin gaggawa saboda hauhawar farashin kayayyaki a duniya, gwamnatin tarayya na aiki cikin matsananciyar matsalar kuɗin shiga da ake samu sakamakon karkatar da albarkatun ƙasa wajen magance rashin tsaro cikin gaggawa a fadin kasar.

“Ina roƙon ku da ku yi la'akari da matsalar kudaden shiga da gwamnati ke fuskanta a halin yanzu, wanda ya samo asali daga ayyukan marasa kishin kasa ta hanyar satar ɗanyen man fetur ɗin mu, wanda ke taimaka mana wajen samun kuɗaɗen shiga,” inji shi.

“An kuma samu ƙara tabarbarewar tattalin arziƙin duniya sakamakon yaƙin Rasha da Ukraine da ake ci gaba da yi, wanda ya haifar da ƙaruwar farashi, ba kawai a farashin kayayyaki da ayyuka a duniya ba, har ma da safarar waɗannan kayayyaki da ayyuka a fadin duniya.  .

Shugaban ya kuma ƙara da cewa cutar Covid-19 ta taka rawa wajen matsin tattalin arziƙin da Najeriya ke ciki.

"Sai lokacin da kasarmu ta samu tsaro ne za mu iya ci gaba da daukar wasu fannoni na kalubalen tattalin arzikinmu," inji Shugaba Buhari.

Shugaban ya kuma bayar da umarnin a gaggauta duba rahoton da Orosanye ya fitar domin gwamnatin tarayya ta aiwatar da shawarar da aka bayar.

Buhari wanda ya bayyana cewa an kusa kammala bitar, ya ce aiwatar da shi zai kawo wasu muhimman sauye-sauye a tsarin ma’aikatan gwamnati.

Rahoton da aka fitar tun a shekara ta 2011, ya kawo cece-kuce tsakanin al'umma, ganin yadda takardar ta bayar da shawara hadewa da soke wasu hukumomin gwamnati sama da 263.

Ta kuma bayar da shawarar soke dokar da ta kafa Hukumar Kula da Ma’aikata ta Kasa da kuma mika ayyukan ta ga hukumar tattara Kudaden shiga da tsare-tsare don cetowa gwamnati Naira biliyan 2.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci