OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Buhari Ya Taya Macron Murnan Sake Lashe Zabe

Buhari Ya Taya Macron Murnan Sake Lashe Zabe

President Muhammadu Buhari and French President, Emmanuel Macron| Photo Source: PM News Nigeria

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya takwaran sa na kasar Faransa Emmanuel Macron murnar sake lashe zabe.

Buhari ya taya shi murna saboda kafa tarihi a matsayin shugaban kasa daya tilo da aka sake zaba cikin shekaru ashirin.

Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawun sa, Garba Shehu a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Buhari wanda ya bayyana Macron a matsayin fitaccen shugaba ya ce salon shugabancin sa na ci gaba da zaburar da sabon salon shugabanci na gari.

Ya kara da cewa dangantaka tsakanin Najeriya da Faransa na ci gaba da samun kyakykyawan tsari tun lokacin da Macron ya hau karagar mulki.

Ya kuma danganta ziyarar da Macron ya kawo Najeriya a shekarar 2018 a matsayin wata kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Ya kara da cewa shugaban da aka sake zaba ya yi kokari wajen kyautata alaka a tsakanin kasashen biyu ta fuskar tattalin arziki da tsaro da kuma al'adu.

Yayin da yake yi masa fatan Allah ya yi masa jagora da bashi hikima, Buhari ya kara tabbatar wa da zababben shugaban kasar goyon bayan Najeriya wurin samar da zaman lafiya da cigaba ta hanyar kirkire-kirkire.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci