OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

NCAA ta dakatar da lasisin jiragen sama masu zaman kansu 3 da suka karya ka'ida

NCAA ta dakatar da lasisin jiragen sama masu zaman kansu 3 d

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta dakatar da lasisin jirage masu zaman kansu uku sanadiyar gudanar da harkokin kasuwanci.

 

Mukaddashin Darakta-Janar na hukumar NCAA, Kyaftin Chris Najomo, ya sanar da dakatarwar a cikin wata sanarwar a wani fefen bediyon da suka wallafa a shafin NCAA na X wanda akafi sani da Twitter a ranar Talata.

 

A cewar Kyaftin Najomo, gudanar da hadahadar kasuwancin da masu lasisin jirage masu zaman kan su sun saba wa tanadin sashi na 9114 na dokokin sufurin jiragen sama na Najeriya.

 

"A watan Nuwamba 2023 ministan sufurin jiragen sama Festus Keyamo SAN, ya bayar da umarnin yin dakatar da masu amfani da jirage masu zaman kansu don kasuwanci"

 

 “Hukumar NCAA ta gargarde su da su guji cigaba da aikata wannan lamarin ta kuma tura jami’anta don sanya ido kan ayyukan tashohin jiragen sama masu zaman kansu a duk filayen jiragen sama a Najeriya sakamakon tsarara matakan an gano akalla wasu kamfanoni masu zaman kansu guda uku da suka sabawa tsarin lasisin su na PNCF". A cewar Kyaftin Najomo.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci