OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Buhari Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa

Buhari Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya  jagoranci taron ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Taron yanzu yana gudana a fadar gwamnati da ke Abuja, kamar yadda wakilin Jaridar Punch ya tattaro.

Akwai tsauraran matakan tsaro yayin da baƙi ciki har da gwamnonin APC ake saran da wuya su samu damar shiga taron.

Hakan ya faru ne a daidai lokacin da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar suka mamaye kofar shiga dakin taro na Banquet Hall.

Ɗakin taron ya samu tsauraran matakan tsaro na ma'aikatan farin kaya da ke kula da fadar shugaban ƙasa.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, a jawabinsa na maraba, ya ce a yayin ƙaddamar da kwamitin, jam’iyyar ta shirya murkushe dukkan ƴan adawa.

Yace jam'iyyar su a shirye take ta take tare da murƙushe babbar jam'iyya mai adawa dama sauran ƙanana ta hanyar samun nasarar a zaɓen baɗi.

A halin da ake ciki kuma, a wajen ƙaddamarwan, shugaba Buhari zai kuma ƙaddamar da shirin gudanar da ayyukan dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci