OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Barde Ya Lallasa Jamilu da Wasu, Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na PDP a Gombe

Barde Ya Lallasa Jamilu da Wasu, Ya Lashe Zaben Fidda Gwani

Alhaji Jibrin Barde| Photo Source: Vanguard

Alhaji Jibrin Barde ya doke Jamilu Isyaku Gwamna da wasu biyar inda ya zama zababben dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Gombe.

Barde ya lashe zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar Laraba da kuri’u 160.

Jamilu Isyaku Gwamna ya samu kuri'u 119 ya zama na biyu a zaben.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, babban jami'in zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP a jihar, Mike Oghiadomhe ne ya sanar da sakamakon.

Sauran ‘yan takara biyar da suka fafata a zaben su ne Dr Ali Gombe da kuri’u 17, Adamu Suleiman ya samu kuri’u 18 yayin da Babayo Ardo ya samu kuri’u 13 sai kuma Gimba Ya’u da kuri’a 1.

Oghiadomhe ya bayyana cewa jimillar kuri’u 328 ne aka kada.

Ya kuma yaba da kokarin jami’an tsaro da ‘yan jarida da ’yan takara da shugabannin jam’iyyar bisa yadda suka gudanar da ayyukansu a duk tsawon lokacin zaben.

Ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su hada kai wajen ganin an samu nasara a zaben 2023 mai zuwa.

Yayin da yake gabatar da jawabin karbar sa, Barde ya ce fitowar sa a matsayin wanda ya yi nasara, ikon Allah ne.

Ya kara da cewa yayin da yake tabbatar da cewa jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2023, zai yi tafiya da dukkan ‘yan takaran.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci