OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Annobar Kwalara: Jihar Gombe Ta Samu Mutuwar Mutane 10

Annobar Kwalara: Jihar Gombe Ta Samu Mutuwar Mutane 10

Biyo bayan barkewar cutar kwalara a jihar Gombe, gwamnatin jihar ta ce kawo yanzu ta samu mutuwar mutane goma.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Habu Dahiru ne ya bayyana haka a yau (Alhamis) a wata ganawa da manema labarai a Gombe.

Kwamishinan wanda ya samu wakilcin babban sakataren hukumar kula da kiwon lafiya matakin farko na jihar Gombe, Dr Abdulrahman Shuaibu ya ce ya zuwa ranar 20 ga watan Satumba jihar ta samu masu cutar guda 236.

Ya lura cewa a cikin 2021 jihar ta sami adadin mutane 2,373 a cikin barkewar cutar guda uku.

A cewar sa: “A bana daga watan Yuni, mun sami bullar cutar kwalara a karamar hukumar Balanga kuma saboda saurin taro shi; ba'a samu haɓakar sa ba. 

“Muna ganin an samu karuwar ruwan sama da ambaliyar ruwa a sassa da dama na jihar wanda hakan ya haifar da barkewar cutar kwalara.

“An samu bullar cutar a unguwanni takwas a fadin kananan hukumomin Balanga, Yamaltu-Deba, Nafada, Funakaye da cikin Gombe.

"Ma'aikatar lafiya ta jihar ta fara aiwatar da ayyukan kiwon lafiya na jama'a cikin gaggawa don rigakafi da shawo kan cutar."

Kwamishinan ya kara da cewa ma’aikatar ta samar da cibiyoyin kula da cutar kwalara 13 a fadin kananan hukumomin biyar da cutar ta shafa domin kula da masu cutar kyauta.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci