OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

An kama mutumin daya kashe mahaifiyarsa a Akwa Ibom

An kama mutumin daya kashe mahaifiyarsa a Akwa Ibom

Rundunar ‘yan sandan Akwa Ibom ta cafke wani mutum mai suna Inyangake James Peter dan shekara 40 bisa laifin kashe mahaifiyarsa mai shekaru 70, Mma-Offiong James Peter.

 

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 4 ga Afrilu, 2024, da misalin karfe 9:00 na safe a kauyen Ikpe Annang da ke karamar hukumar Essien Udim, kamar yadda wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar a ranar Litinin.

 

A cewar sanarwar, wanda ake zargin, Inyangake James Peter, ya amince da aikata kissan, kuma tuni aka mika shi ga hukumar binciken manyan laifuka ta kasa (CID) domin gudanar da cikakken bincike.

 

 Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan CSP Odiko MackDon, ya bayyana a lokacin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa wata murya ce ta rinjayi shi da ya “kashe ta,” shi kuma ya aikata hakan ba tare da yana cikin hayyacinsa ba.

 

Hakazalika, an kama Solomon Asuquo Isaac daga Ikot Obok Nsit a karamar hukumar Nsit Ibom bisa laifin kashe dansa mai shekaru 18 mai suna Iboro Isaac a bara sanadiyar wata rigimar cikin gida.

 

Sanarwar ta kuma kara jaddada yadda rundunar Yan Sandan ta kula da yanda aka samu karuwar ’yan uwa dake kashe 'yan uwansu.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci