OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

An chafke abokin hamayyar Gwamnan Ebonyi bisa zargin sa da hannu a kisan wani mutumi

An chafke abokin hamayyar Gwamnan Ebonyi bisa zargin sa da h

Abokin adawar Gwamna Dave Umahi a zaben yan majalisar dattawa da za a yi a shekara mai zuwa a jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin Najeriya, an kaishi gidan yari bisa umarnin wani alkalin kotun.

 

Wanda aka kama mai suna Linus Okorie, dan takarar jamiyyar Labour Party (LP) ne na gundumar Ebonyi ta Kudu, kuma tsohon dan majalisar wakilai ne.

 

Mista Umahi, wanda wa'adin sa na gwamna zai kare a shekara mai zuwa,wanda a yanzu ya kasance dan takarar kujerar Sanata na jam'iyyar All Progressives Congress.

 

Ana zargin Mista Okorie da hada baki da wasu wajen kashe Wani mutum da kuma yada rikici.

 

An gurfanar da shi ne a ranar Talata a gaban alkali Linda Ogodo, a Abakaliki, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

 

Ana tuhumar sa tare da wasu akan zargin kashe wani mutum mai suna Donatus Okoro.

 

Duk da cewa Rahoton da NAN ta ce har yanzu kotu bata bada takamaimai jawabin irin gudunmuwar da shi Mr Okorie ya bayar wajen aikata kisan ba.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci