OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Tsohon Sakataren Gwamnati, Anyim Ya Gana Da Wakilan Zamfara

2023: Tsohon Sakataren Gwamnati, Anyim Ya Gana Da Wakilan Za

Pius Anyim

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Sanata Anyim Pius Anyim ya gana da wakilan jam'iyyar na jihar Zamfara gabanin zaben fidda gwani na jam'iyyar.

Anyim wanda ya gana da wakilan a Abuja a ranar Alhamis ya yi alkawarin kawo karshen matsalolin tsaro da ake fama da su a jihar idan har ya samu dama.

Ya kasance tsohon shugaban majalisar dattawa a lokacin shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

A lokacin da yake ganawa da wakilan jihar Zamfara, Anyim ya koka kan yadda kashe-kashen da ake yi a jihar da sauran jihohin kasar nan ke karuwa.

Ya kara da cewa, idan aka ba shi damar shugabancin Najeriya, zai yi amfani da dimbin albarkatun kasa da ke jihar, wanda hakan zai sa ta zama jiha mafi arziki a kasar.

Yayin da ya ke bayyana irin yadda zaben 2023 ya bambamta da sauran, ya ce Najeriya na bukatar a hada kai cikin zaman lafiya fiye da baya.

Ya ce, “A gare ni a matsayina na mai neman aiki, duk inda na yi aiki, zaman lafiya na gaba, duk inda na shiga akwai adalci da gaskiya.

“Zan tabbatar da cewa tsaron rayuka da dukiyoyi ya dawo ba jihar Zamfara kadai ba har ma a fadin Najeriya baki daya."

Daya daga cikin wakilai kuma jigo a jam’iyyar PDP a Zamfara, Kanal Bala Mande (Rtd) wanda ya yi magana a madadin wakilan ya bayyana kwarin gwiwar cewa za a iya amincewa da tsohon sakataren muddin aka ba shi dama.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci