OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023 : Rikicin PDP Ya Kara Ta'azzara Yayin Da Magoya Bayan Wike Suka Janye Daga Kamfen din Atiku

2023 : Rikicin PDP Ya Kara Ta'azzara Yayin Da Magoya Bayan W

A safiyar yau laraba a garin Fatakwal magoya bayan Wike sun sha alwashin ba za su shiga hidimar yakin neman zaben Atiku ba har sai Ayu ya yi murabus.

Cif Olabode George, wanda ya fice daga dakin taron shine ya karanto sanarwar a madadin 'yan kungiyar.

“A matsayin mu na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a jam'iyyar PDP bama goyon bayan shugabancin Ayu.

Don haka mun yanke shawarar cewa Sanata Iyorchia Ayu ya yi murabus a matsayin shugaban riko na yankin kudancin Najeriya.

Saboda haka mun yanke shawarar cewa baza mu shiga hidimar yakin neman zabe ta kowace siga ba har sai Dr Iyorchia Ayu ya yi murabus,” inji shi.

A makon da ya gabata dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP Atiku ya kai ziyara jihar Oyo domin ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda aka hangi Gwamna Seyi Makinde, wanda ya kasance makusanci ga Wike, ya sake jaddada cewar dole sai Ayu ya sauka daga kujerar shugabancin jam'iyyar.

Wanda Hakan ya yi sanadiyyar raba kan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a yankin Kudu maso Yamma yayin da akasarin su suka nuna kin amincewar su akan wannan kuduri.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci