OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: PDP Ba Za Ta Yi Nasara A Zaben Shugaban Kasa Ba Tare Da Ni, Da Wasu Gwamnoni Hudu Ba— Wike

2023: PDP Ba Za Ta Yi Nasara A Zaben Shugaban Kasa Ba Tare D

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi alfaharin cewa jam'iyyar PDP ba za ta ci zabe a shekarar 2023 ba tare da sa hannun sa da na wasu gwamnoni hudu daga kudancin Najeriya ba.

 

Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai kai tsaye a garin Fatakwal na jihar Ribas, ranar Jumaa.

 

Jamiyyar PDP ta tsunduma cikin rikicin shugabanci tun bayan zaben fidda gwani na jamiyyar inda tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya doke Wike da sauran 'yan takarar jamiyyar.

 

Rikicin dai ya kara taazzara ne bayan da aka yi watsi da Wike aka ki zaben sa a matsayin abokin takarar Atiku, inda aka zabi gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa.

 

Wike, cikin bacin rai ya zargi jam'iyyar da cin amanarsa da kuma keta kundin tsarin mulkin ta.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci