OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Atiku Zai Kawo Rashin Haɗin Kai Da Ruɗani a Ƙasa – APC

2023: Atiku Zai Kawo Rashin Haɗin Kai Da Ruɗani a Ƙasa �

APC

Jam’iyyar mai mulki ta APC ta ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, zai wargaza Najeriya tare da haddasa rigima mafi muni idan aka zaɓe shi.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a yayin da take mayar da martani ga kalaman da Atiku ya yi a yayin taron tattaunawa kan manufofin yankin Arewa a Kaduna ranar Asabar.

“Abin da talakawan Arewa ke buƙata shi ne wanda ya fito daga Arewa.

"Ba ya buƙatar ɗan takara daga kabilar Yarbawa ko dan ƙabilar Ibo,” in ji Atiku a wani faifan bidiyo na taron.

Da yake mayar da martani a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC, Barista Felix Morka, ya ce abin da Atiku ya ce gagarumin ɓaraka zai kawo ga hadin kan kasa.

“Maganar Atiku babban hari ne ga haɗin kan ƙasarmu. 

"Ya wuce gona da iri a matsayin sa ɗan takara kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasar tarayyar Najeriya, hakan zai tada husuma da rashin haɗin kai a wannan ƙasa.

"Amma ba abin mamaki ba ne dan haka ta fito daga dan takarar da ke neman kujerar shugaban ƙasa ido a rufe.

"Idan kuma kamar yadda Atiku ya yi imani talakan Arewa yana buƙatar Shugaban Arewa a yanzu, bayan Shugaba daga Arewa ya gama,  Menene Atiku yake ganin talakawan Kudu ke buƙata?  

"Me ya sa ake batun abin da talakawan Arewa ke buƙata, ko ma abin da talakawan Kudu ke bukata?

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci