OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

YANZU-YANZU: Rushewar Gini Ya Kashe Mutum Ɗaya a Jigawa

YANZU-YANZU: Rushewar Gini Ya Kashe Mutum Ɗaya a Jigawa

Wani mutum ya mutu a sakamakon rushewar gini da ya auku da sanyin safiyar yau a karamar hukumar Birniwa ta jihar Jigawa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, DSP Lawan Shisu Adam, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:47 na safiyar ranar Asabar.

Rahoton yace wanda abin ya shafa ya mutu nan take yayin da wasu suka samu raunuka, bayan ƴan sanda sunyi gaggawan halartar gurin.

Jami’an ƴan sanda sun garzaya wurin da lamarin ya afku tare da kai wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin garin.

Sanarwar da Jaridar Daily Trust ta ruwaito ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai, yayin da hukumar tace ba su yi zargin wani abu ba saboda ginin an gina shi ne da laka.

Adam yace a baya sun sami rahoton mutuwar mutane bakwai ne yayin da mutum daya ya samu rauni.

Amma daga baya ya kira wakilin su ya tabbatar da cewa mutum daya ne aka tabbatar da mutuwarsa, yayin da sauran mutane shidan da ake tunanin sun mutu ashe suma sukayi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci