OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yan Ta’adda Sun Kashe Mutune 2, Tare Da Garkuwa Da Wasu Da Dama Kan Hanyar Kaduna

Yan Ta’adda Sun Kashe Mutune 2, Tare Da Garkuwa Da Wasu Da

Wasu ‘yan ta’adda sun tare hanyar Birnin-Gwari zuwa Funtua a karamar hukumar Birnin-Gwari dake jihar Kaduna, inda suka kashe mutane biyu tare da yin awon gaba da wasu da dama.

Shugaban kungiyar masu son ci gaban masarautar Birnin-Gwari (BEPU), Ishaq Kasai, a wata sanarwa da ya fitar a  jiya, ya ce ‘yan ta’addan sun kashe wani direba dan kasuwa tare da sace matafiya da dama.

Kasai ya ce, ‘yan bindigar sun tare hanyar ne tun ranar Alhamis da ta yi daidai da ranar kasuwar Birnin-Gwari, inda suka kashe wani direban dan kasuwa tare da yin garkuwa da matafiya da dama.

“Labarai da ke ishe a yanzu na nuna cewa har yanzu matafiya basa iya bi ta hanyar sakamakon yawan garkuwa da mutane da yan fashi keyi.

Kamar yadda yake a yanzu, galibin al’ummomin da ke kan wannan titin kamar Kwasa-kwasa, Marabar Kwasa-kwasa, Nacibi, da Farin Ruwa da dai sauransu, suna bacewa ne saboda fargabar ko wani abu ya faru,".

Kasai, ya kuma kara da cewa, akwai bukatar kara yawan jami'an sojoji a yammacin Birnin-Gwari, musamman a yankin Kakangi da Randagi da ke da iyaka da jihohin Zamfara da Neja, saboda yan bindigar sun kai hari a garin Damari a ranar Asabar da misalin karfe 10 na dare, inda suka kashe mutum daya tare da fasa shaguna da dama dake cikin garin.

Haka kuma, a yayin da yake yaba da sabon kokarin gwamnati da dakarun sojojin, shugaban kungiyar ta BEPU, Ishaq Kasai ya bukaci a tsawaita aikin zuwa maboyar ‘yan ta’addan a cikin dazuzzukan domin dawo da zaman lafiya domin jama’a su zauna a cikin al’ummarsu ba tare da tsoro da fargaba ba.

?TGN    DT

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci