OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

‘Yan bindiga sun kutsa kauyen Filato, sun kashe sarakuna da wasu mutum biyu

‘Yan bindiga sun kutsa kauyen Filato, sun kashe sarakuna d

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Kulias da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Filato inda suka kashe wasu sarakuna biyu da wasu mutane biyu.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na daren Lahadi.

Sarakunan kauyen biyu da aka kashe sun hada da Mataru Mahwash (mai shekaru 67) da Mallan Amalam mai shekaru 50 yayin da sauran biyun aka bayyana sunayen su da Ishaya Fompun mai shekaru 50 da kuma Daniel Ishaya mai shekaru 22.

Daily Trust ta ruwaito cewa wani Josiah da ya rasa babban wan sa a harin ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun kai farmakin ne da yawan su.

Ya kara da cewa harin ya jefa al’umma cikin firgici.

A cewar Josiah: “Maza da yawa dauke da makamai sun kai hari a yankin mu da misalin karfe 9:00 na daren jiya.

“Sakamakon haka, an kashe mutane hudu ciki har da yaya na, Mista Mataru Mahwash.

“Da jin karar harbe-harbe da maharan ke yi, kowa da kowa ciki har da ni suka yi ta tururuwa domin tsira a cikin dazuzzukan da ke kusa da su har sai da aka gama harbe-harben.

“Da dawowar mu, na tarar da yayana da wasu mutane uku a cikin jini.

“Mutanen mu na cikin makoki sosai.

"Ba su da tabbas kan abin da zai same su a gaba."

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta bakin kakakin ta, Alabo Alfred ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce tun daga lokacin ne rundunar ta tura jami’an ta zuwa cikin Kauyen. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci