OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Ministan kudin na Zimbabwe ya bukaci alumma su rungumi amfani da sababbin takardun kudi

Ministan kudin na Zimbabwe ya bukaci alumma su rungumi amfan

Ministan kudi na Zimbabwe, Mthuli Ncube, ya ba da umarnin cewa, a yanzu dole ne dukkan hukumomin gwamnati suyi amfani da kudin da aka samar a baya-bayan nan, saboda rahotannin da ake samu na karancin kudin.

 

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa a ranar Talata. 

 

A cewar sanarwar, kudin na ZiG Gold, wanda aka gabatar a watan da ya gabata, yanzu ya zama halastacciyar hanyar kasuwanci da musayar kudi a cikin kasar kuma bukata da wadatar sa ce zata tanatance darajar kudin a kasuwa.

 

An shawarci dukkan ma'aikatu, da hukumomi (MDAs) da kuma kamfanoni masu zaman kansu su yarda da ZiG a matsayin kudin hukuma don duk hada-hadar kudi.

 

Ministan ya kara da cewa, samar da kudin na da nufin daidaita tattalin arzikin kasar Zimbabwe, wanda ke fuskantar hauhawar farashin kayayyaki. 

 

Sai dai duk da sabbin kudin da aka fara yadawa a karshen watan da ya gabata, ana ci gaba da fuskantar karancin sa a fadin kasar in ji shafin intanet na New Zimbabwe. 

 

Wannan dai shi ne karo na uku da aka amfani da sababbin takardun kudi a Zimbabwe cikin shekaru goma.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci