Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi, ta ce ta samu bizar maniyyata 2,200 a jihar domin gudanar da aikin hajjin bana.
Babban Sakataren Hukumar, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ya bayyana haka a ranar Talata, inda ya kara da cewa jihar na da maniyyata 2,680.
Idris ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da rabon jakunkuna da Unifom ga maniyyatan jihar da aka shirya a hedkwatar hukumar, ya kuma ba da tabbacin hukumar ta himmatu wajen ganin an samar da biza ga sauran maniyyatan a kan kari.
Ya kuma kara da cewa hukumar ta yi dukkan shirye-shirye don fitar da jadawalin tashin jirgin mahajjata.
Jami’in yada labarai na hukumar Muhammad Sani Yunusa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana cewa babban sakataren ya bayyana Uniform a matsayin wata shaida ga dukkan mahajjata a lokacin aikin Hajji.
Ya kuma bukaci alhazai da su rika sanya rigar su a kodayaushe tun daga sansanin Hajjin Bauchi har zuwa lokacin gudanar da aikin Hajji a kasar Saudiyya.
A cewar Yunusa, shugaban hukumar ya shawarci alhazai da su gaggauta dinka rigar su a kan lokaci, yana mai cewa hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta sanya ranar 15 ga Mayu, 2024 don fara jigilar maniyyata zuwa Saudiyya.
0 Tsokaci