OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

NOA ta nemi hadin kan OSSIEC don magance matsalolin da ake fuskanta lokacin zabe

NOA ta nemi hadin kan OSSIEC don magance matsalolin da ake f

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, reshen jihar Osun, ta nemi hadin gwiwa da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Osun, OSSIEC, domin don dakile magudin zabe da tashe-tashen hankula a zaben kananan hukumomin da ke tafe a watan Fabrairu, 2025.

 

 Daraktan Hukumar NOA ta Jiha, Bola Morgan ta bayyana haka a lokacin da ta kai ziyarar neman haddin kai zauwa ofishin Shugaban OSSIEC, Hashim Abioye da ke Osogbo.

 

 Morgan ta bayyana cewa, makasudin ziyarar ita ce ta karfafa alakar da ke tsakanin hukumomin biyu.

 

 Ta ce, “Karfafa wayar da kan jama’a na daya daga cikin ayyukan hukumar mu a wani bangare na wayar da kan ‘yan kasa, muna rokon gwamnati ta sake dawo da Boy's Scout, Boy's Brigade da sauran su a duk makarantun firamare da sakandare." 

 

A nasa jawabin, shugaban kungiyar OSSIEC, Hashim Abioye ya yabawa tawagar hukumar wayar da kan jama’a ta kasa bisa wannan ziyarar, sannan kuma ya taya sabuwar Daraktar hukumar murnar samun sabon mukamin da tayi.

 

Abioye ya yi amfani da wannan damar wajen baje kolin nasarorin da Hukumar ta samu cikin ‘yan watanni da rantsar da shi. Ya tabbatar wa tawagar gudanarwar NOA dorewar kyakyawar  alakar dake tsakanin hukumomin biyu. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci