OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Likitoci sun tabbatar da akalla yan Najeriya 17,000 ne ke kamuwa da cutar kansar mahaifa a duk shekara

Likitoci sun tabbatar da akalla yan Najeriya 17,000 ne ke ka

Nigerian Doctors Relocating to the UK

Dakta Habeebu Muhammad, Babban Darakta a cibiyar ciwon daji a asibitin koyarwa na Jami’ar Legas da ke Idi-Araba, yace akalla yan Najeriya 17,000 ne ke kamuwa da cutar kansar mahaifa a duk shekara. 

 

Likitan ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da jaridar PUNCH Healthwise. “Muna da sabbin masu kamuwa da cutar kansa kusan 102,000 duk shekara, kusan kashi 15 cikin 100 na wannan adadin sun kamu ne da cutar kansar mahaifa” in ji shi. 

 

Likitancin ya fayyace cewa daya daga cikin dalilan farko na mace-macen da ke da alaka da cutar kansa shine jinkirta kai marar lafiya asibiti sai cutar ta riga ta kai wani mataki. Ya lura cewa gano cutar da wuri yana ceton rayuka, yana mai nanata cewa yana da matukar muhimmanci wajen rage mace-macen cutar daji da kuma makudan kudaden da ake kashewa wajen kula da masu cutar.

 

Ya bukaci ‘yan Najeriya da ke da alamun cutar da su nemi taimako da wuri, su kuma yi rayuwa mai inganci domin kare kai daga kamuwa da cutar daji.

 

Ciwon daji na mahaifa, nau'in kansa ne da ke tasowa a cikin mahaifar mace, shi ne na hudu da aka fi samun ciwon daji a tsakanin mata a duniya.

 

A Najeriya, cutar sankarar mahaifa ita ce ta uku da aka fi kamuwa da ita kuma ta biyu mafi yawan sanadin mutuwar ciwon daji a tsakanin mata masu shekaru tsakanin 15 zuwa 44.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci