OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Rundunar Yan sandan Kano ta kama masu chanjin kudi ba bisa ka'ida ba

Rundunar Yan sandan Kano ta kama masu chanjin kudi ba bisa k

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tare da hadin gwiwar hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta kama wasu mutane 17 da ake zargi da chanja kudi ba bisa kaida ba.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Talata. 

 

Sanarwar ta ce, an kai samame ne a ranar 7 ga watan Mayun 2024 a Wappa Bureau De Change da ke karamar hukumar Fagge a Kano. 

 

"A ci gaba da kokarin daidaita kasuwar canji a kasar nan, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sake kai wani samame a wuraren da ake zargi ana chanja kudade ba bisa ka'ida ba. An kama mutane 29, amma an saki 12 saboda rashin isassun shaidu,”

 

 Sanarwar ta kara da cewa, sauran mutane 17 da ake zargin an same su da laifukan da suka hada da, chanja kimanin CFA 68,000 CFA, da rupees din Indiya 30.

 

 A cewar rundunar ‘yan sandan Kano, binciken da aka yi ya nuna cewa wadannan mutane suna gudanar da aiki a karkashin wata “Association of Un Licensed Bureau De Change.” Ya yi nuni da cewa za a gurfanar da su a gaban kotu bisa laifin da ake zarginsu da aikatawa. 

 

Sanarwar ta kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, ya yabawa jami’an bisa wannan nasarar tare da jaddada aniyar rundunar na dakile ayyukan chanja kudaden haram. 

 

"Wannan kame yana aikewa da sako cewa ba za a amince da irin wadannan ayyuka ba, wadanda ke yin su za su fuskanci fushin doka,” inji shi.

 

 Kwamishina Gumel ya kuma bukaci dukkan daidaikun mutane da ‘yan kasuwa da ke cikin harkar hada-hadar kudi da su yi aiki bisa ka’ida tare da samun lasisin da ya dace. 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci