OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji Uku A Zamfara

'Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji Uku A Zamfara

Armed bandits/file copy

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Kaura-Namoda ta jihar Zamfara, inda suka kashe sojoji uku tare da jikkata daya.

Rahotanni sun ce an kai harin ne a daren Laraba.

An yi wa sojojin kwanton bauna ne a lokacin da suke bakin aiki.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ga jaridar Punch ta ce an tura sojojin ne domin dakile harin da ‘yan bindiga suka tsara kaiwa kauyen Kada-mutsa da ke karamar hukumar Zurmi a jihar.

Majiyar ta bayyana cewa ‘yan bindigan sun samu labarin inda suka yi wa motar da ke dauke da sojojin kwanton bauna.

A cewar majiyar: ‘Yan ta’addan sun yi kwanton bauna ne inda suka far wa motar da ke dauke da jami’an sojin, inda suka kashe uku daga cikin su tare da raunata daya."

Majiyar ta bayyana sunan shugaban tawagar da aka kashe a matsayin ‘Manjo Emos’.

Majiyar ta bayyana cewa: “Jami’in soja ne haziki wanda ya sadaukar da rayuwar sa wajen kare rayukan al’ummar karamar hukumar Kaura-namoda.

“Marigayin ya kasance a koyaushe yana amsa kiran gaggawa a duk lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a yankin.

"Mutuwar sa babban rashi ne ba ga al'ummar karamar hukumar Kaura-namoda kadai ba har ma da jihar baki daya."

Sai dai har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ba ta fitar da wata sanarwa ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci