OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Bindiga Sun Kashe Dan Shekara 7, Sun Sace Mutum 10 A Abuja

'Yan Bindiga Sun Kashe Dan Shekara 7, Sun Sace Mutum 10 A Ab

Al’ummar Paikon Basa da ke karamar hukumar Abaji a Abuja sun shiga cikin tashin hankali yayin da ‘yan bindiga suka bindige Ayuba dan shekara bakwai.

‘Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutane 10 daga cikin garin da kuma garin dake makwabtaka da ita. 

AllNews ta tattaro cewa an kai harin ne a daren Juma’a yayin da ‘yan bindigan suka kutsa da manyan makamai.

Da yake tabbatar da rahoton, Daily Trust ta ruwaito cewa wani mazaunin garin James Gwatana ya ce, “Hakika al’ummar Paiko gaba daya sun firgita saboda karar harbe-harbe na ‘yan bindigan. 

"Sakamakon harbin da aka yi a kai-a kai ne ya sa aka kashe wani yaro dan shekara 7."

Rahotanni sun bayyana cewa, wasu mazauna garin ma sun samu raunuka na harbin bindiga, inda daga bisani aka kai su asibiti domin kula da lafiyar su.

Wani basaraken gargajiya a yankin mai suna Abubakar Sardauna da yake tabbatar da faruwar lamarin ya ce wadanda suka samu raunuka an kai su Gwagwalada domin yi musu magani.

A halin da ake ciki kuma, an yi garkuwa da mutane hudu a cikin garin yayin da ‘yan bindigan suka kai farmaki kan shaguna domin neman kayan abinci.

Sai dai basaraken ya bayyana cewa ya samu labarin cewa mutanen hudu sun tsere.

Wata kauye mai suna Mawogi mai tazarar kilomita biyu ita ma 'yan bindigan sun kai hari bayan farmakin da suka fara kaiwa.

An bayyana cewa ‘yan bindigan sun yi awon gaba da wasu mutane shida.

A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ba ta ce uffan ba kan lamarin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci