OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kotun Daukaka Kara Ta Wanke Aderogba Daga Zargin Kisan Kai

Kotun Daukaka Kara Ta Wanke Aderogba Daga Zargin Kisan Kai

Google picture of man in court

Kotun daukaka kara da ke Abuja, a hukuncin daya yanke ranar Litinin, 31 ga watan Oktoba, 2022, ta kori tare da wanke Manjo Akeem Aderogba Oseni daga tuhumar da ake masa na kisan kai. 

 Kotun ta amince da hujjar Ozekhome, cewa rundunar sojin Najeriya ba ta tabbatar da laifin kisan kai da aka yi wa Manjo ba.

 Kotun ta yi mamakin dalilin da ya sa za a yanke wa Manjo Oseni hukunci shi kadai bisa laifin da ake tuhumarsa da shi tare da Wasu kuma wanda ake tuhumarsu duka an sallame shi tare da wanke shi.

An yanke hukuncin farko a ranar 7 ga watan Fabrairu, 2020, inda ta yanke wa Manjo Aderogba hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari. Majalisar Soji ta tabbatar da hukuncin a ranar 24 ga Nuwamba, 2020.

An sallami sauran jami’an biyun da aka kama tare da shi a ranar 24 ga Nuwamba, 2020.

A wata sanarwar daukaka kara mai kwanan wata 28 ga Janairu, 2021 kuma aka shigar a ranar 11 ga Oktoba, 2021,Ozekhome ya shigar da kara shida (6) na daukaka kara a madadin Major Aderogba.

Ozekhome, SAN, ya bayar da hujjar daukaka karar ne a ranar 19 ga watan Satumba, 2022, a gaban kotun daukaka kara, reshen Abuja, a wani kwamitin mutum uku karkashi jagorancin Mai shari’a Stephen Jonah Adah.

Inda a jiya Kotun daukaka karar ta sanar da hukuncin kora tare da wanke Manjo Akeem Aderogba Oseni daga tuhumar kisan kai da za a hukunta a karkashin sashe na 105 (a) na dokar rundunar soji, CAP A20. LFN, 2004.

Sanarwar hukuncin tace "ta samu cancantar daukaka karar, ta amince da shi, sannan ta sallame ta kuma ta wanke Manjo Aderogba daga tuhumar da ake masa"

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci