OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

’Yan bindiga sun kashe dan banga, sun sace dan dan-majalisar dokoki A Sokoto

’Yan bindiga sun kashe dan banga, sun sace dan dan-majalis

Armed Bandits

'Yan bindiga sun kutsa kauyen Rimawa da ke karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto, inda suka kashe wani dan banga mai suna Malam Bakwai.

A yayin harin, ‘yan bindigan sun kuma yi awon gaba da wani dan dan-majalisa mai wakiltar Goronyo a majalisar dokokin jihar, Faruk Ahmadu Rimawa.

Harin wanda ya auku da misalin karfe 4:00 na yammacin jiya (Laraba) ya yi sanadin jikkata wani mutum guda.

Shugaban karamar hukumar, Abdulwahab Goronyo ya tabbatar da hakan a yau.

Goronyo ya ce maharan sun kai farmakin ne a kan babura da misalin karfe 4:00 na yamma.

Goronyo wanda ya zanta da Daily Trust ya ce: “Ni da shugaban jam’iyyar PDP na jihar muna garin Goronyo muna jajanta wa iyalan wadanda suka rasu lokacin da aka sanar da ni harin.

“Na yi gaggawar tattara jami’an tsaro zuwa yankin amma ‘yan bindigan sun tafi tare da yaron kafin isowar su.

“Sun kuma kashe dan kungiyar ‘yan banga guda daya tare da raunata wani mutum guda."

Yayin da rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ba ta fitar da wata sanarwa ba, dan majalisar ya ce wadanda suka yi garkuwa da dan nasa sun tuntube shi amma ba bu wata bukata.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci