OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Bindiga Sun Kai Wa Maniyyata Aikin Hajji Hari A Sokoto

'Yan Bindiga Sun Kai Wa Maniyyata Aikin Hajji Hari A Sokoto

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wasu maniyyata aikin hajji da ke kan hanyar zuwa Sokoto daga karamar hukumar Isa ta jihar.

A cewar rahoto, maniyyatan suna shirin tashi ne a yau (Talata) da karfe 7:30 na safe.

Harin wanda aka kai jiya a dajin Gundumi, jami’an tsaro da ke tare da ayarin maniyyatan ne suka dakile shi.

Daily Trust ta ruwaito wani mazaunin garin Isa mai suna Malam Sirajo ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ba a samu asarar rai ko jikkata ba.

Ya ce, “Sun kai wa ayarin motocin su (maniyyatan) hari, wanda jami’an tsaro ke rakiyar su, wadanda aka ce sun yi artabu da ‘yan bindigar na wasu mintuna.

"Mun sami labarin cewa wasu daga cikin jami'an sun samu raunuka, wanda ba zan iya tantancewa ba."

Duk da cewa babu wani rahoton sace mutane da aka yi, babban sakatare a hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Sokoto, Shehu Muhammad Dange, ya ce an kai harin amma bai iya tantance yanayin maniyyatan 21 daga karamar hukumar ba.

A halin da ake ciki rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Ahmad Rufa’i ta ce rundunar ba ta da masaniya kan harin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci