OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yajin Aiki Ba Gudu Ba Ja Da Baya – Direbobin Legas

Yajin Aiki Ba Gudu Ba Ja Da Baya – Direbobin Legas

Kungiyar direbobin Najeriya JDWAN reshen jihar Legas, a ranar Juma’a, ta ce a shirye take tsunduma yajin aikin gargadin da suka ayyana na kwanaki bakwai da za su fara a ranar Litinin, 31 ga Oktoba, 2022.

 Direbobin hadin gwiwar sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai, wanda aka gudanar a gidan Right, dake Ikeja, a jihar Legas.

 Wadanda ake sa ran shiga yajin aikin da ke tafe sun hada da direbobin kananan bas (Korope), motocin bas na gwamnatin tarayya Mass Assisted Transit, Mazda Buses, T4, LT, Ford.

 A nasa jawabin, shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Akintade Abiodun, ya ce yawan harajin da ’yan gareji da jami’an tsaro suka yi wa direbobin hadin guiwa ya haifar da hauhawar farashin kayayyakin abinci a Legas idan aka kwatanta da sauran jihohi. 

 Da yake jawabi yayin taron manema labarai, babban Lauyan direbobin, Ayo Ademiluyi, ya ce yajin aikin ya zama dole domin nuna rashin amincewa da yadda mambobin kwamitin kula da gareji da wuraren shakatawa na jihar Legas a karkashin jagorancin Musiliu Akinsanya da aka fi sani da MC Oluomo, suke tsawalawa direbobin haraji.

 A cewarsa, direbobin sun yi asarar fiye da rabin abin da suke samu ga ’yan daba ta hanyar tsatsaura musu a gareji da tashoshin mota ko sun dauko fasinjoji ko basu dauka ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci