OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban matasan jam’iyyar APC a Enugu

Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban matasan jam’iyyar A

Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban matasan jam’iyyar APC a karamar hukumar Igbo-Eze ta Kudu a jihar Enugu.

Marigayin mai suna Lucky Idoko ya fito ne daga unguwar Unadu da ke yankin karamar hukumar.

Ya na wakiltan al'umman ne a matsayin Kansila.

Shugaban matasan, wanda shi ne shugaban kungiyar ‘yan banga na yankin, an harbe shi ne a ranar Asabar, a lokacin da yake tafiya a kan babur din haya.

An ce wanda ke tuka babur din ya yi nasarar tsallake rijiya da baya.

Wasu majiyoyi sun ce ana ta cece-kuce a yankin cewa lallai wannan lamari wasu ne suka masa ture.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe, ya tabbatar da faruwar lamarin.

“Rundunar ‘yan sandan ta kaddamar da bincike a kan kisan Lucky Idoko,” inji shi.

Lamarin ya faru ne awowi kadan da wasu ‘yan bindiga su ka kai hari a hedikwatar ‘yan sanda da ke karamar hukumar Oji ta jihar.

An kashe mutane biyu ciki har da dan sanda a harin da aka kai a ofishin 'yan sanda.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci