OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Fasinjoji 13 Sun Ƙone Ƙurmus Dalilin Hatsarin Mota A Enugu

Fasinjoji 13 Sun Ƙone Ƙurmus Dalilin Hatsarin Mota A Enugu

Aƙalla fasinjoji 13 ne suka ƙone ƙurmus a wani mummunan hatsarin da ya afku a kusa da unguwar Four Corners Enugu a daren Lahadi.

Rahotanni sun bayyana cewa motar bas mai dauke da kujeru 14 da ta tashi daga jihar Imo zuwa Adamawa ta ci karo da tirela kafin ta kama wuta.

An ce dukkan fasinjojin banda guda ɗaya sun ƙone ƙurmus a hatsarin da ya afku a karshen titin Enugu da Patakwal.

Fasinja ɗaya ne ya tsira daga hatsarin motar, kamar yadda rahotanni mabanbanta suka ruwaito.

Yayin da wasu ke cewa wasu mutane ne waɗanda suka tausayawa waɗanda abun ya afka musu suka cecesu.

Yayin da wasu kuma ke cewa mutumin ya fice ne daga motar ne ya gudu.

Wanda ya tsira a halin yanzu yana samun kulawa a sashin gaggawa na asibitin koyarwa na jami’ar Najeriya UNTH, Ituku-Ozalla.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe tara na daren Lahadi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci