OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Za a sake kamo dubunnan fursunonin da suka tsere, cewar Aregbesola

Za a sake kamo dubunnan fursunonin da suka tsere, cewar Areg

Dubunnan fursunonin da suka tsere daga gidajen gyaran hali na Najeriya za a sake kama su ko nan da shekara nawa ne.

Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi a wani hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya,ta yi dashi “NAN Forum.”

A hirar wanda aka buga a yau lahadi, Mista Aregbesola bai bayar da takamaiman lokacin da za a sake kama fursunonin ba.

“Sai dai su gudu amma baza su iya, ɓoye mana ba; kamar beran da aka danawa tarko haka suke za mu kamo su,” in ji Mista Aregbesola.

PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa kimanin mutane 4,000 da suka tsere daga gidan yarin suna nan a cikin kasar nan Wadanda suka aikata laifin sun hada da ‘yan ta’adda da sauran wadanda aka samu da laifukan tashin hankali.

Gidajen yarin da aka yi tashe-tashen hankula sune na Abuja,Oyo da kuma jihar Edo.

A cikin hirarsa, Mista Aregbesola ya yi tsokaci kan yadda za a sake kama fursunonin.

“Za su bude asusu a banki; za su yi amfani da lambobin waya; yaudarar kansu kawai suke yi; za a kama su,” inji shi.

“Kamar beran da aka sawa tarko haka suke. Beran da aka sa wa tarko in zai je ? Zaka sake sa ya yi shawagin sa lokacin da kaga dama sai ka damke sa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci