OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Aregbesola Ya Nemi A Sake Fursunoni Kashi 30 A Gidan Gyaran Hali Saboda Cunkoso

Aregbesola Ya Nemi A Sake Fursunoni Kashi 30 A Gidan Gyaran

Ministan harkokin cikin gida, Mista Rauf Aregbesola, ya ce zai gana da gwamnonin jihohi domin cimma matsaya kan sakin aƙalla kashi 30 na fursunonin da ake tsare da su a fadin ƙasar.

Aregbesola ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata a yayin da taron kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Abuja.

Ministan ya ce, hanyar sadarwa ta zama dole domin sama da kashi 90 cikin 100 na fursunonin ana tsare da su ne saboda sabawa dokokin jihar.

Yayin da ya ce sama da kashi 70 cikin 100 na fursunoni 75,635 a halin yanzu suna jiran shari’a.

Aregbesola ya ce masu laifin gwamnatin tarayya bai kai kashi 10 cikin 100 ba, inda ya ce galibin mutanen da ake tsare da su ne wadanda suka saba dokokin jihar.

Ya ce saboda haka ana ci gaba da tsare su a ƙarƙashin ikon jihohinsu, cewar Jaridar Punch.

"Na rubuta wa ƙungiyar gwamnonin Najeriya domin su ba ni dama in zo in yi musu jawabi kan yadda za su tallafa wajen rage cunkoso.

“Saboda dole ne gwamnoni su goya mana baya a wannan tsarin domin mu yi gagarumin rage cunkoso musamman na fursunonin da suke jiran shari’a.

"Idan muka samu goyon bayan hukumomin shari'a na jihohi da gwamnatin jihohi, za mu iya fitar da kashi 30 cikin 100 na waɗanda ke tsaren."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci