OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sojojin Najeriya Sun Aika 'Yan Ta'adda 36 Lahira A Yankin Arewa Maso Gabas

Sojojin Najeriya Sun Aika 'Yan Ta'adda 36 Lahira A Yankin Ar

Sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai sun aika ‘yan ta’adda da dama lahira a cikin makonni biyu da suka gabata a yankin Arewa maso Gabas.

Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan a yau (Alhamis) a Abuja.

A cewar sa, sojojin sun kuma kawar da wasu manyan kwamandojin Boko Haram da na ISWAP guda biyu.

Ya bayyana sunayensu da Abu Asiya da Abu Ubaida A’Qaid.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Danmadami ya ce: “Saboda haka, a cikin lokacin da aka bayyana, sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 36, ​​sun ceto fararen hula 130 tare da kama mutane 46 da ake zargin ‘yan ta’addar Boko Haram ne da kuma 12 da ake zargin suna bayar da labarin sirri ga ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP. 

“Bugu da kari, an kwato bindigogi kirar AK47 guda 21, harsasai 163 na 7.62mm na musamman, bama-baman RPG guda biyu, bindigogin gargajiya guda 25, akwatin bama-bamai guda hudu, na’urorin hasken rana 10, kekuna 23, babura 10 da keke Napep guda daya. 

“Sauran kayayyakin da aka samu sun hada da, wayoyin hannu 19, fitulun tocila 28, buhunan hatsi iri-iri, tumaki 122, da kudi N203,125 da dai sauran su."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci