OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sojoji Sun Turmushe ‘Yan Bindiga, Sun Kubutar Da Mata Shida da Jariri A Kaduna

Sojojin Najeriya sun samu nasarar turmushe 'yan bindiga a maboyar su da ke karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

Sojojin sun kuma kubutar da wasu mata shida ciki har da wani jariri yayin aikin sharan fage.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.

Aruwan ya bayyana cewa sojojin sun ci gaba da aikin sharan fage a wurin a halin da ake ciki. 

A cewar kwamishinan, sojojin na Operation Forest Sanity ne suka kai farmakin a safiyar ranar Talata.

A cewarsa: “Bayan sun share sansanin, sojojin sun ceto wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su a wurin.

“Wadanda aka ceto sune: Sahura Hamisu, Ramlatu Umar, Saudatu Ibrahim, Maryam Shittu, Fatima Shuaibu, Khadijah Mohammed tare da jaririnta.”

Ya kara da cewa wadanda aka ceto din tuni aka hada su da iyalan su.

“Gwamnatin jihar Kaduna ta lura da rahoton, musamman ma ceto ‘yan kasa guda shida da aka yi garkuwa da su, tare da godiya.

“Gwamnati ta yaba wa sojoji, ‘yan sanda, jami’an leken asiri, ‘yan banga da sauran jami’an tsaro, bisa nasarar da aka samu a wani zagaye na gudanar da ayyukan,” in ji Aruwan.

Gwamnatin jihar Kaduna ta kara jinjina wa sojojin bisa hobbasa da suka yi wanda ya yi sanadiyar samun nasarar aikin.

A cewar Kwamishinan: “Rundunar tsaro za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a yankin baki daya da sauran wuraren da abin ya shafa a fadin jihar. Za a ba da rahoton ƙarin bayani daidai da haka," kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci