OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sojoji Sun Kawar da Ƴan Ta’adda Sama Da 250 S Arewa Maso Gabas

Sojoji Sun Kawar da Ƴan Ta’adda Sama Da 250 S Arewa Maso

Sama da 'yan ta'addan Boko Haram 252 ne sojojin Operation Hadin Kai suka fatattaka a cikin makonni biyu da suka gabata a yankin Arewa maso Gabas.

Daraktan yada labarai ta fannin tsaro Manjo janar Musa Danmadami,ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai na mako biyu kan ayyukan soji a fadin kasar, wanda ya gudana a ranar Alhamis a Abuja.

Danmadami ya ce an samu wannan nasarar ne a wasu farmaki da sojin sama da na kasa suka kai a yankunan kauyukan jihohin Borno da Yobe.

Ya ce daya daga cikin hare-haren an kashe ‘yan ta’adda 52, sannan kuma an kama wasu 14 tare da kubutar da uku daga cikin ‘yan matan Chibok da aka sace Jinkai Yama, Falmata Lawal da Asabe Ali.

A cewarsa, an kubutar da su a wurare daban-daban tare da ‘ya’yansu da kuma wasu mutane 19 da aka sace.

“Sojoji sun kuma kwato gurneti guda biyu da bai fashe ba, bindigogin AK47 guda 12, bindigogin FN guda uku, AK47 guda biyar, na’urar harba gurneti guda daya da kuma bam din hannu daya.

“Kazalika an kwato ma’adinan AP guda 86, harsashi 7.62mm, babur daya, kwari da baka u 16, kekuna bakwai da wayoyin hannu guda 10.

“Haka zalika, an kama wani da ake zargin dan kasar waje ne mai sayarwa da 'yan ta'adda kayayyaki da kuma dillalin makamai ga ‘yan ta’addar, mai suna Mallam Abatcha Bukar, da allurai iri-iri, na'urar cire rasit guda 2 da kuma kudi N294,520,” inji shi.

Mista Danmadami ya kuma ce dakarun sa ido na sirri sun kama wani dan ta’addan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, Mamuda Usman wanda aka fi sani da Bado a yankin Asokoro da ke babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce, an bayyana cewa wanda ake zargin ya kai wa wani babban kwamandan ‘yan ta’adda aika ne a Kaduna.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci