OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 42 yayin da 3,858 suka mika wuya

Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 42 yayin da 3,858 suka mika

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kashe 'yan ta'addar Boko Haram 42 a yankin Arewa maso Gabashin kasar cikin makonni biyu da suka gabata.

Sanarwar ta fito ne daga bakin Darakta mai kula da harkokin yada labarai na tsaro, Manjo-Janar Bernard Onyeuko a Abuja ranar Alhamis.

Onyeuko ya bayyana cewa a kalla 'yan ta'adda 3,858 ciki har da manyan kwamandoji shida ne suka mika wuya ga sojojin Najeriya.

Ya bayyana kwamandojin da suka hada da Malam Mala Hassan (Wali), Ali Madagali (Munzur), Musa Bashir (Cif Anur), Buba Dahiru (Munzur), Jafar Hamma (Kaid) da Abbali Polisawa.

Ya ce an samu nasarar ne a lokacin da sojoji suka kai farmakin maboyar ‘yan ta’addan.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito, Onyeuko ya bayyana cewa rundunar sojin sama na Operation Hadin Kai ta kawar da ‘yan ta’adda sama da 21 a Tumbum Jaki da Tumbum Murhu kusa da tafkin Chadi a jihar Borno a ranar 11 ga watan Yuli.

Ya ci gaba da cewa, ‘’yan ta’addan Boko Haram 3,858 da iyalan su ne suka mika wuya tsakanin 1 ga watan Yuli zuwa 14 ga watan Yuli, wadanda suka hada da maza 505, mata 1,042 da yara 2,311.

Kakakin rundunar ya kara da cewa sojoji sun samu nasarar cafke masu hada kai/masu kai wa 'yan ta'addan kayayyaki a wurare daban-daban.

Ya ce: “A cikinsu akwai mata biyu; Hauwa Gambo da Khadija Dirsa."

Ya kara da cewa, "Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 42, sun kama 10, sun kwace bindigu AK47 guda 17, bindigar QTC daya, bam RPG 1, bututun RPG daya, gurneti guda biyar, zagayen harsashi 120 na 5.5mm da zagayen harsashi 54 na musamman 7.62mm."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci