OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Siyar Da Ganuwar Kano Ya Ragewa Sashin Yawon Bude Ido Armashi — Lajawa

Siyar Da Ganuwar Kano Ya Ragewa Sashin Yawon Bude Ido Armash

Ganuwa

Siyar da ganuwar Kano na daga abinda ke dakile ci gaban wuraren shakatawa a jihar tare da ragewa sashin armashi ga masu son ziyarar su.

Shugaban hukumar kula da yawon bude ta jihar Kano, Yusuf  Ibrahim Lajawa ne ya sanar da haka yau Talata, yayin bikin ranar yawon bude ido da shakatawa ta duniya  da akan gudanar kowace 27 ga Satumba.

Yace akwai alfanun gaske wajen ci gaban yawon bude idanu ga kowace jiha, don haka ne ma ya bukaci al’ummar Kano da su rika bawa hukumar goyan baya domin bunkasa yawon bude idon.

Da yake jawabi yayin taron, shugaban hukumar yawon bude ido shiyya ta daya na kasar nan, Alhamdu Bako ya ce bullar Covid-19 ya kawowa bangaren koma baya sosai.

Ya bukaci aluma su bayar da hadin kai wajen alkinta ababen tarihi wanda hakan zai bunkasa yawon bude ido a jihar, tare da kira ga gwamnatoci su yi hubbasa wajen cicciba sashen.

Bikin yawan bude ido da shakatawar da ya gudana a wannan rana a harabar hukumar, ya samu halartar mutane da dama daga sassan kasar nan, wanda aka kammala da kade-kade da hukuma gasar wasa kwakwalwa tsakanin wasu daliban makarantun jihar Kano.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci