OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Shugaban hukumar shige da fice ya ziyarci iyalan jami’in da ‘yan ta’adda suka kashe a Jigawa

Shugaban hukumar shige da fice ya ziyarci iyalan jami’in d

Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice ta Najeriya Isah Jere, a ranar Asabar, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan jami’in shige da ficen da aka kashe da wadanda suka jikkata a wani artabu da akayi da ‘yan ta’adda a karamar hukumar Maigatari ta Jihar Jigawa.

 Yankin karamar hukumar Maigatari yanki na kan iyaka tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Wasu ‘yan bindiga a kan babura sun kai hari kan tawagar jami’an shige-da-fice da ke sintiri a yankin a ranar 9 ga watan Agusta inda suka kashe jami’i Abdullahi Mohammed, tare da raunata wasu biyu Abba Musa da Zubairu Garba.

Lamarin ya faru ne a kewayen Galati-Birniwa,mai tazarar kilomita 70 daga hedikwatar karamar hukumar.

Mista Jere ya shaida wa manema labarai cewa hukumar shige da fice na alfahari da sadaukarwar da jami’in da ya rasa ransa ya yi da kuma sauran jami’an biyu da suka jikkata.

“Na zo jihar Jigawa ne domin in ziyarci jami’ai na da mutane na domin mika ta’aziyya ta ga iyalan Abdullahi Mohammed, babban mataimakin jami’an shige-da-fice, hazikin mutumi wanda ya sadaukar da rayuwar sa a lokacin da yake bakin aiki wajen kare lafiyar ‘yan yankin mu."

"Na zo Jigawa ne domin in yaba da kuma girmama irin sadaukarwar da wannan ma'aikaci na mu ya yi wajen kare martabar yankin mu da kasa baki daya."

"Abdullahi Mohammed ya kasance daya daga cikin fitattun jaruman mu, jarumi kuma babban mai kishin kasa.

"Ina tabbatar wa dangin sa cewa dan su bai mutu a banza ba.

"A madadin Jami’ai na da ni, muna yi masa addu'an Allah jikan sa ,” in ji Mista Jere.

Mista Jere ya ce jin dadin jami’an hukumar shige da fice na daya daga cikin abubuwan da ya sa a gaba.

"Ina bayyana muku cewa, jin dadin ma'aikata shine babban buri na.

"Muna tabbatar da cewa jami’an mu sun samu kyakykyawan kima, da daraja a hidimar kasa."

"Ina so in bayyana cewa kudurinmu na tabbatar da tsaron iyakokin kasarmu ba abu ne da ake tattauna akai ba".

Za mu ci gaba da ba da kyakkyawar kariya a kan iyakoki mai kilomita 5037 don haɓaka zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

“Muna yin sabbin hanyoyin zamani don tsaron kan iyaka da suka hada da tura kadarori don inganta ingantaccen tsaro da sarrafa kan iyakoki."  

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci