Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya bayar da umarnin rufe makarantun sakandare a fadin jihar saboda barkewar cutar kyanda.
Shugaban riko na hukumar kula da makarantun gaba da firamare na jihar Adamawa Samuel J. Wagereng ne ya bayar da wannan umarni a ranar Litinin.
Sanarwar ta ba da umarnin a ci gaba da rufe dukkan makarantun har zuwa ranar Litinin 13 ga Mayu, 2024.
allnews.ng ta tattaro cewa makarantun sun bukaci daliban su da su dawo a yau 6 ga watan Mayu 2024 domin cigaba da karatu kamar yadda aka saba saidai sanarwar ta dage komawar zuwa sati mai zuwa.
Wani bangaren sanarwar yace "Ya kamata makarantu su kasance a rufe har zuwa mako mai zuwa ranar Litinin 13/5/2024 saboda barkewar cutar kyanda a fadin jihar, wannan umarni ya hada har da makarantu masu zaman kansu"
Idan za'a iya tunawa Allnews.ng ta rawaito a ranar Juma’a ne aka tabbatar da mutuwar mutane 42 daga kamuwa da cutar kyanda a kananan hukumomi biyu na jihar.
Kwamishinan lafiya da ayyukan jin kai na jihar, Felix Tangwami wanda ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Yola, babban birnin jihar ya bayyana cewa ma’aikatar ta samu rahoton mutum 131 sun kamu da cutar a Mubi da kuma 177 a kananan hukumomin Gombi.
Ya ce: “Barkewar ta shafi mazaba 8 a Mubi da mazabu 7 a Gombi inda adadin wadanda suka mutu ya kai 42 dag acikin 131.
0 Tsokaci