OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Hukumar ICPC ta bukaci Masu yiwa kasa hidima su tallafawa wajen kakkabe cin hanci da rashawa

Hukumar ICPC ta bukaci Masu yiwa kasa hidima su tallafawa wa

An hori masu yiwa kasa hidima NYSC da su tallafawa wajen kakkabe cin hanci da rashawar daya dabbaibaye kasar nan. 

 

Winifred Ngobro, wakiliyar hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, ce ta yi wannan kiran a sansanin horar da masu yi wa kasa hidima dake Ede a jihar Osun.

 

 Ngboro wanda ke jawabi ga mambobin Batch A Stream II da aka tura jihar ta yi karin haske kan rawar da ICPC ke takawa wajen tunkarar al’amuran da suka shafi cin hanci da rashawa a tsakanin al’umma.

 

 A cewarta, “manyan ayyukan ICPC sun hada da aiwatar da doka, binciken laifukan da kuma gurfanar da wadanda ake zargi.Ta kuma mai da hankali kan kokarin hada kai da nufin samar da sauyi a tsakanin matasa"

 

Ta kara da cewa "Ina rokon ku da ku yi amfanin da shafin yanar gizon ICPC din turo mana bayanai kan wadanda kuke zargi da karya ka'ida, ICPC.gov.ng."

 

 Ngboro wanda ta yi kira da a hada kai a yaki da cin hanci da rashawa ta lura cewa yana da matukar muhimmanci wajen gina al’umma mai gaskiya da rikon amana.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci