OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da kisan Sheik Aisami na jihar Yobe

Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da kisan Sheik Aisami na ji

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyyan sa ga iyalan babban malamin da wani soja ya hallaka a jihar Yobe,inda ya umurci rundunar soji da suyi gaggawar hukunta wanda ya aikata wannan aika-aika

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa malamin nan na jihar Yobe, Goni Aisami.

Rundunar ‘yan sanda ta ce sojan mai suna John Gabriel, wanda malamin ya ragewa hawa, a motar sa ya amsa laifinsa na kashe malamin a kokarinsa na son kwace motar sa.

Ana tuhumar Mista Gabrial da wani mai suna Adamu Gideon bisa laifin fashi da makami da kuma kisan kai.

A wata sanarwa da mai taimaka ma Shugaban Kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, Mista Buhari ya ce irin wannan aika aika bai dace da soja ba, kuma ya saba wa ka’idar sojoji.

Don haka ya bukaci shugabannin sojoji da su fatattaki miyagun sojoji da ke cikin su.

"Wannan kisan gillar da wannan Soja ya aikata ba ya cikin tarbiyyan mu a matsayin mu na sojoji, kuma hakan ya saba wa duk wani salon rayuwar soja wanda ya ginu kan ladabtarwa da kuma girmama rayukan wadanda basu ji ba ba su gani ba."

“A matsayina na Babban Kwamanda, wannan lamarin ya fusata ni ,wannan mugun aiki da jami’in tsaro ya aikata a matsayin sa na wanda aka horar da su don kare rayukan jama'a.

"Horon da aka ba mu, muna bin ka’idojin da’a da suka saba wa irin wannan rashin hankali tare da kauce aikata laifuka.

"Ba dabi'ar mu ba ce cutarwa da 'yan kasa da basu ji ba ba su gani ba. Tabbas, Laifin da wannan soja ya aikata shi daya na iya zama bakin fenti ga sauran sojoji.”

“Wannan lamarin na iya sanya ‘yan kasar mu su ji tsoron taimaka wa sojoji, wanda hakan na iya ruguza amincin da ke tsakanin sojojin mu da farar hula.

"Saboda haka ina kira ga hukumomin soja da su hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki ba tare da bata lokaci ba, tare da kawar da masu irin wannan dabi’a,” Cewar shugaba Buhari.

Shugaban ya mika ta’aziyya ga gwamnatin jihar Yobe da al’ummar jihar da kuma iyalan mamacin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci