OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Shugaba Buhari ya Taya Goodluck Murnar Cika Shekara 64

Shugaba Buhari ya Taya Goodluck Murnar Cika Shekara 64

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Dr Goodluck Ebele Jonathan| Hoto Daga: Daily post

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasar Najeriya, Dr Goodluck Ebele Jonathan murnar cika shekaru 64 da haihuwa.

Shugaban ya kuma yaba masa bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen samar da zaman lafiya da cigaban dimokuradiyya a nahiyar Afirka.

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Femi Adesina, mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai.

Shugaban ya ce Dr Jonathan ya zame wa mutane da yawa kwarin gwiwa tare da gogewar sa kan shugabanci da sauransu.

Ya kara da cewa, a yayin da tsohon shugaban kasar ya rike mukamin mataimakin gwamna, gwamna, mataimakin shugaban kasa, shugaban kasa, wakilin kungiyar tarayyar Afirka kuma a yanzu ya zama shugaban kungiyar International Summit Council for Peace Africa (ISCP-Africa), mutane da dama sun yi koyi da shi.

Kungiyar ISCP-Afrika kungiya ce ta tsoffin shugabannin kasashe masu ci da mataimakansu.

Kungiyar Zaman Lafiya ta Duniya ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta kafa kungiyar a shekarar 2019.

Ya kuma bukaci mutanen da ke neman mukaman shugabanci da su yi koyi da tsohon shugaban kasar wanda zuciyarsa ta bauta wa mutane ce.

Buhari ya kuma yi addu’ar Allah ya kara wa tsohon shugaban kasar lafiya tare da mika gaisuwar sa ta musamman.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci