Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya amince da takarar Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa na jam’iyyar PDP.
Atiku shine ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyar da kuma mataimakin sa a takarar Ifeanyi Okowa a zaɓen 2023 mai zuwa.
Jonathan ya bayyana haka ne a lokacin da tawagar PDP ƙarƙashin jagorancin Okowa da kuma Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi suka kai masa ziyara a Abuja, a yammacin Laraba.
A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Jonathan ya bayyana Gwamna Okowa na jihar Delta a matsayin mataimakin shugaban Najeriya mai jiran gado.
Ya kuma bayyana cewa a shirye yake ya bawa jam’iyyar PDP goyon baya ɗari bisa ɗari
Sa'annan ya kuma yace zaiyi aiki domin samun nasarar jam’iyyar PDP a zaben 2023, cewar Jaridar Punch.
Mista Jonathan a ƙarshe ya yi wa ƴaƴan jam’iyyar fatan samun nasara a dukkan al’amuransu.
Da yake daga hannun Okowa, Jonathan ya ƙira shi "Mataimakin Shugaban ƙasa mai jiran gado."
Da yake bayani, Gwamna Okowa ya ce yana da muhimmanci a nemi goyon bayan shugaba Jonathan da albarkar sa.
0 Tsokaci